Taron wanda aka gudanar a birnin Nice da ke gabashin kasar, ya samu halartar manyan jami’an jam’iyyar da suka hada da tsohon Firaminista Jean-Pierre Raffarin wadanda suka nuna alamun goyon baya ga Sarkozy.
Daya daga cikin manyan jami’an jam’iyyar kuma dan Majalisar Dokoki da ke wakiltar yankin na Nice Christian Estrosi, ya ce suna bukatar a dawo da tsohon shugaban kasar domin jagorantar jam’iyyar. ABNA